Kofin Duniya: Bashir El-Rufai ya Bukaci Hukumomin Qatar da su Halaka Duk Wanda Aka Kama da Giya a Kasar

 

Bashir El-Rufai, ‘Dan gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya shiga kanun labarai sakamakon wata wallafa da yayi wacce ta janyo cece-kuce.

A wallafar da yayi a Twitter, ‘dan Gwamnan ya bukaci hukumomi a Qatar da su kama, gurfanar tare da halaka duk wanda aka kama da giya a kasar.

Wannan wallafar tashi kuwa ta janyo maganganu kala-kala yayin da wasu suke caccakarsa bayan fara gasar kwallon kofin duniya a kasar Musuluncin.

Bayan dokoki masu tsauri da aka saka kan giya a gasar kwallon kafa ta kofin duniya a Qatar, Bashir El-Rufai, ‘dan Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya bayyana matsayarsa kan lamarin.

A ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamban 2022, Bashir ya je shafinsa na Twitter inda ya bayyana goyon bayansa kan haramta shan giya da hukumomin Qatar suka yi yayin gasar.

Kamar yadda wallafarsa da Legit.ng ta gani a Twitter tace:

“Ina fatan a kama, gurfanarwa tare da halaka duk wanda aka samu ya shigar da giya filin wasan kasar da take da dokokin hani kan hakan.”

Jama’a sun yi martani

Jim kadan bayan wannan wallafar, jama’a sun fusata da ita inda wasu suke kallonsa da maras son zaman lafiya tare da munafunci.

@realchado yace:

“Mutum zai goyi bayan Qatar kan kiyaye al’adarta amma kuma Bashir ‘dan El-Rufai yayi fatan halaka bakin haure kan giya. Ko da a ce ‘yan kasa ne, babu wani ladabtarwa ne baya ga wannan tsohon yayin? Dole ne kowanne laifi ya zama hukuncinsa kisa ne?

@KunleBoye yace:

“Cire kai? Ana kiranka da barawo amma kana rawa da akuya a hannu?”

@nmatopclass:

“Kisan tsoka ba shi ne bane kisa. Ana cewa, idan kaje gari ka gansu da bindi, kaima nema ganye ka saka. A mutunta al’adar jama’a.”

@emmaneul_yours:

“Halaka mutum saboda ya shigar da giya filin wasa? Mun gode Allah kan cewa mutanen da aka fara aikowa da addinin Musulunci ba kauyawa bane kamar ka wanda kawai ke kwafar wani sashe na addinin.

“Babu shakka, hakan yasa kiyasin cigaban jama’a a arewacin Najeriya har yanzu yake kasa.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here