Bata Gari Sun Saka Bam a Babbar Kasuwar Izombe da ke Jihar Imo

 

Wasu tsageru da ake tsammanin mambobin IPOB ne sun ta da babbar kasuwar Izombe yayin da mutane suka fito kasuwanci a Imo.

Maharan da ake zaton masu tilasta bin dokar zaman gida ne sun kona motoci biyu kuma suka jefa Bam a cikin kasuwar.

Yan kasuwan da suka fita don harkokin su na kasuwanci sun yi matuƙar firgita, wasu da dama kuma sun jikkata.

Imo – A ranar Litinin wasu miyagun yan bindiga suka tada bama-bamai a Babbar kasuwar Izombe da ke ƙaramar hukumar Aguata, jihar Imo, yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Premium Times ta rahoto cewa ana zaton yan bindigan mambobin haramtacciyar ƙungiyar yan aware ne wato IPOB waɗan da ake zargin suna tilasta mutane bin dokar zaman gida kowace Litinin.

Bayanai sun nuna cewa tun farko maharan sun je kasuwar domin su gargaɗi mutane kar su yi yunkurin taka dokar ta hanyar fitowa kasuwanci, a ruwayar jaridar Sun.

Amma sai yan kasuwan suka yi kunnen uwar shegu da gargaɗin suka fito domin gudanar da harkokin kasuwancin su na yau da kullum, hakan ya tunzura yan ta’addan suka farmake su.

Rahoton ya ƙara da cewa sai da ‘yan bindigan suka ƙone motocin biyo kafin daga bisani suka harba bama-bamai a harabar kasuwar.

Ya mutanen da ke kasuwanci suka yi?

Yan kasuwan da suka riga da suka fita gudanar da harkokin kasuwancin su sun firgita da harin, inda suka yi takansu domin tsira da rayuwarsu.

Wasu daga cikin yan kasuwan da dama sun jikkata yayin harin amma babu rahoton wani ya rasa rayuwarsa.

Wani shaidan da lamarin ya auku a kan idonsa ya shaida wa Jaridar cewa:

“Suna zuwa suka fara jefa Bam cikin kasuwar kuma nan take kowa dake ciki ya fara neman hanyar tserewa. Haka nan maharan sun zuba man Fetur kan wasu motoci biyu, ko ina da komai ya yi kaca-kaca a kasuwar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here