Rashin Kwarewar Hadiman Buhari ya Bata ma Shugaban Kasar Suna da Mutuncinsa – Laori Kwamoti

 

Dan majalisa, Laori Kwamoti, ya ce hadiman Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun mayar da Najeriya abun dariya.

Kwamoti ya ce rashin kwarewar hadiman Buhari ya bata ma Shugaban kasar suna da mutuncinsa.

Dan majalisan ya yi gargadin cewa Najeriya ba za ta ci gaba ba har sai an dauki kwararru don kula da Shugaban kasar da gwamnatinsa.

Laori Kwamoti, wani dan majalisan Adamawa mai wakiltan mazabar Numan/Lamurde/Demsa a majalisar wakilai, ya koka kan yadda hadiman Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke bata masa suna.

Dan majalisan ya bayyana matsayarsa a ranar Talata, 12 ga watan Janairu, a garin Yola, inda ya kara da cewa hadiman Shugaban kasar sun yi barna sosai a gwamnatinsa.

A cewarsa, furuci mara ma’ana da martanin mafi akasarin masu kula da harkokin labaran Shugaban kasar ya “rage darajar Najeriya zuwa abar dariya.”

Kwamoti, wanda ya kuma bayyana cewa Najeriya na daukar wasu mutane da hukumomi a matsayin wadanda suka fi karfin doka, ya yi gargadin cewa kasar za ta ci gaba da komawa baya idan aka ci gaba da mulkin kama karya, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Ya kara da cewa kada yan Najeriya su yi tsammanin kowani sauyi mai kyau daga gwamnati mai ci har sai Buhari ya kawo mutane masu mutunci da tunani.

“Ku duba wannan batu; Shugaban kasar ya fada ma duniya cewa zai gurfana a gaban majalisar dokokin tarayya, kawai sai ga wasu hadimai marasa kwarewa sun fito suna fadin cewa mu (yan majalisar tarayya) bamu da ikon gayyatar Shugaban kasar. Shin wannan ba abun kunya bane?

“A kasar daa mutane suka fi karfin kotuna, yan sanda, sojoji da sauran hukumomin da sune ginshikin damokradiyya babu inda za a je; za ta ci gaba da kasancewa koma baya.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here