Wasu Bata Gari Sun Kai Hari Ofishin ‘Yan Sanda, An Rasa Mutane 2
Rundunar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kai kan ofishin yan sanda a jihar Edo.
An tattaro cewa an aiwatar da aika-aikan ne a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba.
A cewar rahoton, rundunar yan sandan ta dakile harin sannan ta kashe yan bindiga biyu Wani rahoto daga jaridar This Day ya nuna cewa akalla mutane biyu ne ake zaton sun mutu lokacin da wasu yan bindiga suka kai hari ofishin yan sanda a yankin Igueben, karamar hukumar Igueben na jihar Edo.
Legit.ng ta tattaro cewa yan bindigan wadanda suka aiwatar da harin a daren ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, sun kuma tsere da makamai da harsasai.
Kafin afkuwar lamarin, an rahoto cewa yan bindiga sun yi awon gaba da Fedrick Shaibu, dan uwan mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.

Read Also:

Jaridar ta ce an kashe wani Inspekta na yan sanda da wani karamin jami’i a yayin harin yayinda wasu da dama suka jikkata.
An tattaro cewa maharan sun kai mamaya ofishin yan sandan da misalin karfe 8:00 na dare, suka jefa nakiya a harabar kafin suka iya shiga.
A bisa rahoton, harin ya haddasa gagarumar zanga zanga a yankin yayinda matasa suka fito unguwanni domin kira ga gwamnati a kan ta binciki lamarin.
Da yake martani, kakakin yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor ya karyata batun mutuwar jami’an yan sandan biyu.
Nwabuzor ya ce: “A ranar 9 ga watan Nuwamban 2020, da misalin karfe 19.30hrs, wasu yan iska da ake zaton masu fashi da makami ne sun kai mamaya ofishin yan sanda a Igueben.Nan take, yan sandan suka dakile su.”