Bawa Jahohi Ikon Kafa ‘Yan Sandan su Zai Kara Tabarbarewar Matsalar Tsaro a kasa – Gwamna Zulum

 

Gwamna Babagana Zulum na jahar Borno ya ce baya goyon bayan kafa ‘yan sandan jahohi a Nigeria.

Farfesa Zulum ya ce kafa ‘yan sandan jahar zai bawa wasu gwamnonin damar cin zarafin mutane da basu kauna.

Zulum ya yi wannan jawabin ne a makarantar koyon dabaru da tsare-tsare, NIPSS, da ke Kuru a jahar Plateau.

Plateau – Babagana Zulum, gwamnan jahar Borno ya ce bayan goyon bayan kafa ‘yan sandan jahohi a Nigeria, The Cable ta rawaito.

Ana ta kiraye-kirayen cewa a bawa jahohi daman su kirkiri ‘yan sandansu a wasu jahohin domin magance matsalar tsaro.

A watan Yuli, kudirin neman kafa yan sandan jahar ya wuce karatu na biyu a majalisar wakilai na tarayya.

Onofiok Luke, dan majalisar tarayya daga jahar Akwa Ibom ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisa a cewar rahoton na The Cable.

Amma Zulum ya ce bawa jahohi ikon kafa ‘yan sandan su zai kara tabarbarewar matsalar tsaro a kasar.

Gwamnan Bornon ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da mukallarsa a cibiyar koyan dabaru da tsare-tsare ta NIPSS da ke Kuru, Jahar Plateau.

Da ya ke bayani kan matsayarsa, gwamnan ya ce Nigeria ba ta kai matsayin da za a kafa ‘yan sandan jahohi ba. Ya ce wasu gwamnonin na iya amfani da su domin cin zarafin wasu mutanen ko kabilu.

A cewar Zulum:

“Maganar gaskiya, Ni Babagana Zulum, ba zan goyi bayan hakan ba, ba wai don bana son shi ba, amma saboda abubuwan da za su biyo baya.

“Nigeria ba ta kai matsayin kafa yan sandan jahohi ba, wasu gwamnonin za su iya amfani da su domin kawar da wasu kabilun daga jaharsu.

“Don haka ya kamata mu yi takatsantsan. Idan aka dauki rabin ikon da ke hannun sojoji aka bawa yan sanda da yan sandan jahohi, Nigeria za ta shiga matsala.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here