Bayan Kamuwa da Cutar Korona: Tsohon Kwamishina a Jahar Edo ya Rasu

Mutanen jahar Edo sun tashi da alhinin mutuwar dan su, tsohon kwamishina a jahar, Didi Adodo.

Ya rasu ne da safiyar Talata, 12 ga watan Janairu bayan fama da cutar COVID-19 na kwanaki.

Adodo ya rike kujerar kwamishinan kwadago da ayyuka na musamman lokacin mulkin Adams Oshiomhole.

The Nation ta ruwaito yadda Kwamared Didi Adodo, tsohon kwamishinan kwadago da ayyuka na musamman na jahar Edo ya rasu.

Shugaban kwadagon ya mutu ne da safiyar Talata, 12 ga watan Janairu, bayan fama da cutar COVID-19 na tsawon kwanaki.

Tsohon kwamishinan ya rike kujerar sakataren ISSSAN kafin rasuwarsa. Adodo dan Iruekpen ne, karamar hukumar Esan ta yamma dake jahar, kuma ya rike kujerar kwamishina na tsawon shekaru 8, lokacin mulkin Adams Oshiomhole.

Tun bayan bullowar cutar korona a Najeriya a farkon shekarar da ta gabata, cutar tana cigaba da lamushe rayukan jama’a.

Ta fara lafawa a kwanakin baya amma cikin kwanakin nan mugunyar cutar tana cigaba da hauhawa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here