Ba za a yi Zabe a Cibiyoyi 240 ba a Jihohi Biyar na Najeriya – INEC
Hukumar zabe ta Najeriya ta ce ba za a yi zabe a cibiyoyi kusan 240 ba a jihohi 28 a kasar lokacin zabukan da ke tafe, ranar 25 ga Fabarairu da kuma 11 ga watan Maris.
Shugaban hukumar, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a yau Litinin lokacin da yake ganawar da ya saba da shugabannin jam’iyyu 18 masu rijista, a Abuja.
Read Also:
Shugaban ya ce dalilin hakan kuwa shi ne babu wani mai zabe da ya yi rijista a wadannan cibiyoyi 240.
Ya ce cibiyoyin da ba za a yi zaben ba suna jihohin Zamfara da Kwara da Edo da Rivers da kuma Imo wadda tafi yawansu da 38.
Farfesan ya ce bayan cibiyoyin 240 da ba za a yi zaben ba, duka sauran cibiyoyi kusan 176,606 a fadin kasar za a yi zabe.
Hukumar ta kuma yi gargadin cewa ba za ta amince da yanayin da jam’iyya daya za ta tura wakili fiye da daya ba a cibiyar zabe, su haddasa rudani ba, tana mai cewa duk wakilin da aka samu yana haka za a kama shi a gurfanar da shi gaban shari’a.