An Bayar da Belin Akanta Janar na Najeriya, Ahmed Idris
Jaridu a Najeriya na bada rahoton sakin Akanta Janar na gwamnatin Tarayya, Ahmed Idris, da hukumar EFCC ta kama kan zargin hannu a rashawar naira biliyan 174.
A daren Laraba ake cewa an bayar da belinsa kuma ya koma gida wajen iyalansa.
Kakakin EFCC, Wislon Uwujaren, ya tabbatar da sakin Akanta Janar din ga jaridar Punch ta Najeriya.
Read Also:
Tun a ranar 16 ga watan Mayu, EFCC ta kama Ahmed Idris kan waɗaka da kuɗaɗen a fari ake cewa sun kai naira biliyan 84.
Kwanaki uku bayan cafke shi, Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta sanar da dakatar da shi domin ya fuskanci binciken da ake yi a kansa.
A lokacin da ake tsare da shi akwai rahotanni da ke cewa, Ahmed Idris ya bankado wasu sunaye da kamfanonin da aka yi wa wannan badakala da su.