2023: Gwamna Yahaya Bello ya Magantu a Kan Wanda ya Kamata ya Gaji Shugaba Buhari

 

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya magantu a kan wanda ya kamata ya mallaki tikitin takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023.

Bello ya ce jam’iyyar mai mulki na bukatar kwararren dan takara wanda zai dora daga inda Shugaba Buhari ya tsaya.

Mai neman takarar shugaban kasar ya ce kada a yi la’akari da yankin da mutum ya fito idan har ya cancanta.

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, na bukatar dan takarar shugaban kasa wanda zai gyara albarkatun kasar ba tare da la’akari da yankin da ya fito ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 28 ga watan Maris, a wata hira da Channels TV yayin da ake tsaka da kira ga a mika shugabancin ga yankin kudancin Najeriya.

Ya ce:

“Abin da yan Najeriya ke bukata shine kwararren dan takara, jajirtacce, mai tunani da wayo wanda zai gyara kasar ba tare da la’akari da yankin da ya fito ba.

“Mun ga shugabancin bi-da-bi a kasar nan a baya kuma mun ga sakamakon shi. Abun da yan Najeriya ke bukata shine mutumin da zai ba da wannan fatan.”

A cewar shi, kasar na bukatar shugaban kasa wanda zai hada kan dukka yankin Najeriya sannan ya dora daga inda Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya.

Rahoton ya nakalto Yahaya na cewa:

“Abun da jam’iyyar ke bukata a yanzu shine mutum mai hankali, wayayye kuma matashi wanda zai kwato shugabanci.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here