Gwamna Ben Ayade ya Sallami Kwamishinoni 4 da Hadimansa 5
Gwamnan jahar Cross River, Ben Ayade, ya sallami kwamishinoni 4 da hadimansa 5 bayan komawa APC.
Duk da gwamnan bai sanar da dalilinsa na yin hakan ba, ya mika godiyarsa ga tsoffin kwamishinonin da hadiman.
Kwamishinonin da ya sallama sun hada da na lamurran mata, habaka sabon birni, yada labarai da sauransu.
Gwamnan jahar Cross River, Ben Ayade, ya sallami kwamishinoninsa hudu bayan sauya sheka da yayi daga jam’iyyar PDP zuwa ta APC mai mulki kasa da makonni biyu.
Read Also:
Mai baiwa gwamnan shawara ta musamman a fannin yada labarai, Christian Ita, ta sanar a wata takarda da ta fitar a ranar Litinin a garin Calabar, babban birnin jahar, Daily Nigerian ta tabbatar.
Kamar yadda takardar tace, kwamishinonin da lamarin ya shafa sun hada da Mike Usibe (Kwamishinan sabon birni), Rita Ayim (Kwamishinan harkokin mata), Asu Okang (Kwamishinan yada labarai) da Ntufam Etim (Kwamishinan sauyin yanayi).
Ayade ya kara da sauwakewa hadimansa biyar mukaminsu. Hadiman sun hada da: Leo Inyambe, Orok Duke, Victor Okon, John Bassey, da Mbeh Agbiji.
Kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito, duk da gwamnan bai bada dalilinsa na sallamarsu ba, ya mika godiyarsa ga kwamishinonin da hadiman kan ayyukan da suka yi wa jahar kuma yayi musu fatan alheri.
Legit.ng ta ruwaito yadda Ayade ya sanar da hukuncinsa a ranar Alhamis, 20 ga watan Mayu a wani taro da yayi da gwamnonin APC shida wadanda suka kai masa ziyara har gidan gwamnatinsa.