Joe Biden ya Ziyarci Ukraine
Shugaban Amurka, Joe Biden na wata ziyara a Kyiv – wanda shi ne ziyararsa ta farko tun bayan da Rasha ta mamayi Ukraine kusan shekara ɗaya da ta wuce.
A jawabinsa, Biden ya yaba wa Ukraine bisa jajircewarta a yaƙin da take yi da Rasha, inda ya ce ya taɓa kawo ziyara a Kyiv har sau shida lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa.
Read Also:
“Putin ya ɗauka Ukraine bata da karfi kuma kan ƙasashen yamma a rabe yake…ba ya so ya ga kan mambobin Nato a haɗe. Sannan ba ya son mu kawo taimako ga Ukraine.
“Ya ɗauka zai ci galaba a kan mu. Amma bana tsammanin yana tunanin haka a yanzu. Ya tafka kuskure.”
Tun da farko, ya yi alkawarin bai wa Kyiv sabon taimakon soji da ya kai $500m wanda za a sanar a gobe.
Shugaba Zelensky ya yi maraba da wannan ziyara mai tarihi da shugaban na Amurka ya kai wa ƙasarsa.