Kungiyar IS ta Saki Bidiyon Mutane 20 da ta yi wa Kisan Gilla a Borno
Ƙungiyar IS ta wallafa wani bidiyo da take ikirarin kashe fararen hula 20 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ƙungiyar ta masu tayar da ƙayar bayar da ke ayyukanta a yankin da sunan ISWAP ta ce mutanen da ta nuna ta kashe a bidiyon “kiristoci” ne.
Har yanzu hukumomi ba su ce komai ba akan bidiyon.
Read Also:
Bidiyon wanda ƙungiyar ta wallafa a intanet ya nuna kaso uku na mutane daban-daban a kayan fararen huka – da ke nuna mutum huɗu da 11 da kuma mutum biyar a kowace tawaga, kuma dukkansu maza ne.
Sannan ga alama a wurare daban-daban mutanen suke – waɗanda ƙungiyar ta ce duka a jihar Borno ne.
Babu tabbas kan lokacin da aka ɗauki bidiyon.
Bidiyon ya nuna ƴan ƙungiyar da fuskarsu a rufe ɗauke da bindigogi kuma mai magana da yawunsu yana wulwula wuƙar da ke hannunsa.
Da yake magana da Hausa, mutumin ya ce sun kashe mutanen ne don ramuwa ga kashe shugabanninsu biyu da aka yi a yankin Gabas Ta Tsakiya a farkon shekarar nan.
BBC ba ta iya tabbatar da ikirarin mutanen ba a karan kanta na cewa mutanen kiristoci ba ne, ko kuma inda ainihin abin da ya farun.