Bikin Kirsimati da Sabuwar Shekara: FRSC ta Baza jami’anta a Sassa Daban-Daban

 

Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya FRSC, ta sanar da aike jami’anta a sassa daban-daban na kasar domin sintiri a tituna a lokacin bukukuwan Kirismeti da na sabuwar shekara da ke tafe.

A jawabin da mukaddashin shugaban hukumar , Dauda Biu ya yi wa manema labarai a ranar Litinin, ya ce jami’ansu 36,224 ne za su yi wannan aikin.

Sai dai ya ce hukumar na bai wa ‘yan Najeriya tabbacin kare lafiyarsu da dukiya a lokacin da ake wannan murna ta ganin karshen shekarar 2022 lafiya da fatan ganin 2023 da ke tafe.

A Najeriya dai ana yawan samun hadurran motoci a manya da kananan titunan kasar, musamman lokacin bukukuwan karshen shekara.

Hukumar kiyaye hadurra ta kasar da ‘yan sanda na dora alhakin hadurran ababen hawan kan tukin ganganci, ko gudu fiye da kima da direbobi ke yi, sai kuma rashin hakurin masu ababen hawa a lokacin da aka samu cunkoun ababen hawa.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here