Rundunar Sojin Sama ta Kashe ‘Yan Bindiga a Zamfara

 

 

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce hare-hare ta sama da ta ke kai wa maboyar ‘yan bindiga sun hallaka gwammansu a jihar Zamfara da ke arewacin kasar.

Samame ta sama da sojin suka kai karamar hukumar Maru a karshen mako, ya biyo bayan munanan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kauyukan da ke yankin.

Mazauna kauyukan da ke yankin sun shaidawa BBC cewa matsawar jami’an tsaron Najeriyar ta tilastawa ‘yan bindigar da ke garkuwa da mutane, arcewa wani kauye mai suna Mutunji, inda nan ma akai muu luguden wuta.

Mazauna kauyukan sun kuma ce, sun ga gawawwakin ‘yan bindigar har guda 60, da wasu 20 da suka jikkata, sai kuma baburan maharan da sojojin suka lalata.

Sai dai sun ce akwai tsirarun farar hula da lamarin ya rutsa da su, ciki har da wau tsofaffi da ke kokarin tserewa a lokacin da gungun ‘yan bindigar akan babura da manyan makamai suka tunkaro kauyensu domin gujewa samamen da luguden wuta ta saman da sojojin Najeriyar ke yi babu kakkautawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here