Ziyara Garin Igboho: Alliance For Oke-Ogun Development ta Nemi DSS da ta Binciki Sheikh Gumi

 

Wata kungiya mai suna Alliance for Oke-Ogun Development ta nemi hukumar DSS da ta binciki dalilin ziyarar da Sheikh Gumi ya kai jahar.

Ta yi zargin cewa ziyarar Shehin Malamin wani yunkuri ne na mayar da yankin na Fulani.

A makon nan ne Gumi ya ziyarci garin Igboho, mahaifar mai fafutukar kasar Yarbawa, Sunday Igboho.

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Alliance for Oke-Ogun Development, a yankin Oke-Ogun na jahar Oyo, ta yi kira ga hukumar DSS da ta binciki dalilin ziyarar da Sheikh Ahmad Gumi ya kai garin Igboho.

Mai fafutukar Yarbawa, Cif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho dan asalin garin Igboho ne, hedkwatar karamar hukumar Oorelope ta jahar Oyo.

Jagoran kungiyar ta AOD na kasa, Cif Abiodun Fasasi, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis ya yi zargin cewa ziyarar Gumi wani yunƙuri ne na mayar da yankin Oke-Ogun na Fulani.

Kungiyar OAD ta yi ikirarin cewa ‘yan ta’adda na tserewa daga Arewa maso Gabas bayan nasarar da Sojojin Najeriya suka samu a kan su, jaridar Punch ta rawaito.

Kungiyar ta yi kira ga sarakunan gargajiya a yankin da su yi taka tsantsan da yan cikin gida wadanda, a cewarsu a shirye suke su mika kai ga ‘yan ta’adda bori ya hau.

Ta kara da cewa:

”Abin da ya fi tayar da hankali shine cewa wani dan Oke Ogun na iya karbar bakuncin mutum kamar Gumi, muna son DSS ta binciki ainihin dalilin ziyarar tasa; dole ne a binciki wanda ya sauke shi. Mutumin shi ne wanda aka dora wa alhakin jagorantar kira ga yiwa ‘yan bindigar afuwa.”

“Babban kungiyar zamantakewa ta Oke Ogun, Alliance For Oke Ogun Development, suna amfani da wannan damar don kira ga Gwamnatin Tarayya, Babban Jami’in Tsaro na Jahar Oyo, Gwamna Seyi Makinde, don duba wannan lamari.

“Muna kuma kira ga sarakunan gargajiyar mu da daukacin jama’ar jahar da su kasance cikin shirin ko -ta -kwana kan bakin da ka iya haifar da hadari ga lafiyarmu.”

Sai dai jaridar ta ce a lokacin da aka tuntubi Gumi, a kashe lambobin wayarsa suke kuma bai amsa sakon tes da aka aika wayarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here