Majalisar Wakilai za ta Binciki NAGWW Kan Kashe N81bn Wajen Dashen Itatuwa a Arewa
Hukumar kula da shirin dashen itatuwa wanda aka fi sani da Great Green Wall Project na fuskantar bincike kan yadda ake zargin ta kashe naira biliyan 81 domin dashen bishiyoyi miliyan ashirin da ɗaya a jihohin arewa da ke kan iyakar Najeriya.
Kwamitin majalisar wakilan Najeriya ne ke gudanar da binciken, a kan yadda aka yi amfani da asusun raya muhalli da alkinta yanayi da wasu kuɗaɗen asusun.
Jihohin sun haɗa da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa da Bauci da Gombe da Adamawa da Yobe da kuma Borno.
Daraktan Hukumar ta NAGWW, Yusuf Maina Bukar, ya shaida wa kwamitin cewa hukumar ta kashe naira miliyan 697.71 wajen gyara ofishinta da kuma naira biliyan 11.28 don gudanar da manyan ayyuka.
Read Also:
Ya ƙara da cewa galibin kuɗaɗen da hukumar ke samu, sun fito ne daga kashi 15 cikin ɗari na kuɗaɗen asusun alkinta yanayi da muhalli da kuma waɗanda gwamnatin tarayya ke samarwa.
Baya ga wannan ma, kwamitin ya kuma binciki Babban Bankin Najeriya game da wasu asusun ajiya fiye da bakwai da bankin ya san da su.
Wasu takardun bayanai masu shafuka shida ɗauke da kwanan watan 22 ga Agustan 2023 da bankin na CBN ya miƙa wa kwamitin sun nuna cewa an sakawa asusun hukumar kusan naira biliyan 9 da rabi, tun daga 2015 zuwa wannan ranar.
Babban akantan Najeriya, Oluwatoyin Madein ya bayyana cewa Hukumar kula da shirin dashen itatuwa da alkinta yanayi ta NAGWW ɗin ta ƙarbi kuɗin da yawansu ya zarce naira biliyan 19 tun daga watan Fabrairun 2019 kawo yanzu.
Shugaban kwamitin binciken na majalisar wakilai ta ƙasa, Isma’ila Haruna Dabo tare da sauran mambobin kwamitin sun nuna damuwa kan yadda aka kashe kuɗaɗen babu kan gado.
Kwamitin ya bayyana cewa ya zama wajibi su gudanar da cikakken bincike kan wannan batu duba da irin maƙudan kuɗaɗe da hukumar ke samu daga gwamnatin tarayyar Najeriya da ma sauran ƙasashen waje amma ta sauka daga kan turbar da aka ɗora ta a kai.