Za a Binciko ‘Yan Sandan da Aka Gani a Bidiyo Suna yi wa Matashi ƙwace – IGP Usman Baba

 

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya bayar da uamrnin ƙaddamar da bincike kan ‘yan sandan da aka gani a bidiyo waɗanda aka zarga da yi wa wani matashi ƙwace.

Cikin bidiyon da ya karaɗe shafukan zumunta a jiya Asabar, ana iya jin wanda ke ɗaukarsa na cewa ‘yan sandan sun tsare matafiya ne inda suka zaƙulo wani matashi ɗauke da kwamfuta suka cusa shi a motarsu.

Kazalika ya yi zargin cewa ‘yan sandan sun nemi ya ba su kuɗi amma ya ce ba shi da su a matsayinsa na ɗalibi. Duk da haka suka ce ya buga waya a turo masa ta banki domin su cire a na’urar ATM.

Mai maganar ya ce lamarin ya faru ne a garin Okene na Jahar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.

Cikin wata sanarwa da kakakin ‘yan sanda na ƙasa Frank Mba ya fitar, “IGP Usman Baba ya umarci rundunar reshen Jahar Kogi da ta ƙaddamar bincike nan take”.

“IGP ya buƙaci a kwantar da hankali, yana mai cewa za a tabbatar da adalci da zarar an kammala binciken sannan a gurfanar da ‘yan sandan da aka kama da laifi a gaban kotu,” in ji sanarwar.

A lokuta da dama, ana zargin ‘yan sandan Najeriya da cin zarafin ‘yan ƙasa, abin da ya jawo gagarumar zanga-zangar EndSars a ƙarshen 2020 wadda ta yi sanadiyyar rushe rundunar SARS ta ‘yan sandan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here