Coci ta ba ni Dala 300 Bayan na yi wa Mata 3 Fyaɗe da Kashe su – Matashi

 

Wani mutum da ya amsa yi wa mata uku fyaɗe kafin ya kashe su ya zargi wata coci a Kiambu da ke ƙasar Kenya da ba shi umarnin hakan, a cewar rahoton jaridar Nation.

Paul Magara Morara mai shekara 29, ya yi iƙirarin cewa cocin ta biya shi dala 300 lokacin da ya kashe wani.

Yanzu haka ana tsare da shi a Ofishin ‘Yan Sanda na Ruiru da ke yankin Kiambu a Kenya.

Ya ƙara da cewa cocin ta ba shi dala 300 bayan ya kashe matan uku.

“Abokina ne ya kai ni cocin a shekarar da ta wuce. Za a biya ka dala 300 duk lokacin da ka kashe mutum kuma an faɗa mani cewa mata sun fi sauƙin kashewa,” in ji Morara a lokacin da sashen binciken laifuka ke magana da shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here