Firaministan Birtaniya, Boris Johnson ya yi Gargaɗin Kan Taron COP 26

 

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya yi gargaɗin cewa muddin taron sauyin yanayi na COP 26 a Glasgow ya gaza to komai ma zai wargaje.

Mista Johnson ya ce babu wani uzuri mai gamsarwa da zai sa jan ƙafa wajen samar da matakan shawo kan sauyin yanayi.

Ya ce, tuni aka ga irin matsalolin da sauyin yanayi ya haifar a duniya.

“Mun samu ci gaba a taron G20 mai muhimmanci amma har yanzu akwai sauran aiki. Mun san cewa muna da fasaha, abin da muke bukata shi ne mu tara kuɗi,” a cewar Mista Johnson.

Tun da farko, Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya ce “me ya sa kowacce kasa ba za ta iya rage gurɓatacciyar iskar da take fitarwa gaba ɗaya ba zuwa 2050,” inda ya ce Rasha za ta cika alkawarin da ta dauka zuwa 2060.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here