Hukunci Bisa Kuskure: Za’a Biya Mutumin da ya Kwashe Shekaru 28 a gidan Yari N3.7bn

Daga bisani gaskiya ta yi halinta kuma na tabbatar da adalci a kan wata shari’ar bakar fata a Amurka.

Bisa kuskure aka yankewa Chester Hollman III hukuncin kisa sakamakon kisan wani mutum a yayin da yake da shekaru 21 a duniya.

A yanzu bayan ya kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku an gane ba shi da laifi kuma za a biya shi N3.7bn a matsayin diyya.

Wani mutum dan asalin Philadelphia ya samu ‘yanci a karo na biyu a rayuwarsa kuma ya koma cikin mutane bayan kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku. Chester Hollman III an yanke masa hukunci ne bisa kuskure kuma aka yanke massa hukuncin kisa duk da ba shi da laifi. Amma kuma bayan shekaru 28 da aukuwar lamarin, an gane cewa bashi da laifi kuma an yanke hukuncin biyan shi N3.7bn a matsayin diyya.

Chester mai shekaru 21 ya kasance direba. An kama shi wata rana a tsakar garinsu inda aka zargesa da hannu a cikin fashi da makamin da yayi sanadiyyar rayukan jama’a.

A 2020, alkali ya wanke Chester sannan ya bada umarnin biyansa N3.7bn na irin halin da aka jefa shi ciki da bata masa lokacin rayuwarsa da aka yi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here