Yadda ‘Yan Boko Haram Suka Hallaka Wasu Manoma

Rahoton Premium Times na nuna cewa wasu da kae zargin yan Boko Haram ne su hallaka manoman shinkafa 44 a jihar Borno.

A cewar rahoton, sun hallaka manoman ne yayinda suke girban amfanin gona a Zabarmari.

Majiyoyi a rahoton sun bayyana cewa an “zagaye manoman ne kuma yan bindigan suka yi musu yankan rago,” Hassan Zabarmari, tsohon shugaban manoman shinkafa a jihar Borno, ya bayyana ta wayar tarho.

Ya kara da cewa: “An kai wa manoman hari ne a gonan shinkafan Garin-Kwashebe, kuma bisa rahoton da muke samu da ranan nan, kimanin 40 cikinsu aka kashe.”

Amma muna samun wasu rahotanni daban kan adadin wadanda aka kashe – wasu sun ce manoman da aka yanka sun kai 50.”

Tushe : Legit

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here