Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun kashe Wasu Mutane Tare da Kona Gidaje

 

Wasu yan bindiga sun kai farmaki wani gari a karamar hukumar Jemaa da ke jihar Kaduna.

Maharan sun kashe mutum bakwai, sun raunata hudu sannan suka kona akalla gidaje hudu.

Harin na zuwa ne kimanin kwanaki hudu bayan yan fashi sun kashe wasu mutane hudu a Kaduna.

Jihar Kaduna ta shiga juyayi bayan wani harin sassafe da aka kai sannan aka kashe akalla mutane bakwai a kauyen Ungwan Bido da ke karamar hukumar Jemaa.

Channels TV ta ruwaito cewa wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba wadanda suka far na kauyen a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba sune suka kaddamar da harin.

Har yanzu ba a ga wasu yara biyu ba bayan mummunan al’amarin yayinda maharan suka raunata mutum uku da kona gidaje hudu.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, wanda ya tabbatar da lamarin ya kuma bayyana cewa harin ya biyo bayan rahoton kisan wani Isiyaka Saidu.

An kashe Saidu wanda ya kasance makiyayi a kauyen Ungwan Pah a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.

A halin da ake ciki, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi martani kan sabon harin sannan yayi Allah-wadai da lamarin.

Yayinda yake jaje ga iyalan mamatan da wadanda aka raunata, gwamnan ya umurci hukumomin tsaro da su yi bincike da kamo dukkanin masu hannu a ta’asar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here