Bayan Zuwan Sababbin Hafsoshin Tsaro Borno: ‘Yan Boko Haram Sun Kai Hari a Jahar

Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari Chabal da wasu anguwannin Magumeri dake jahar Borno.

Al’amarin ya faru ne a ranar Lahadi wanda yayi sanadiyyar mutuwar ‘yan sanda biyu tare da sace biyu.

Sun kuma banka wa motocin sintiri biyu wuta da kuma wani a kan hanyar Maiduguri-Chabal -Magumeri.

Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun afka Chabal da wasu anguwanni dake karkashin karamar hukumar Magumeri a ranar Lahadi da rana sannan sun kashe wasu ‘yan sanda guda biyu kafin su yi garkuwa da wasu biyu.

Kamar yadda wasu suka sanar da Vanguard, ‘yan ta’addan sun kwace wasu motocin sintiri guda biyu sannan suka banka wa daya wuta a hanyar Maiduguri-Chabal-Magumeri titi mai tsawon 35km arewa da babban birnin jahar.

Al’amarin ya faru ne bayan sababbin hafsoshin sojin Najeriya da sun kai ziyara Maiduguri, inda suka kai wa gwamnan jahar Borno, Babagana Zulum ziyara da Shehun Borno, Abubakar Garbai Elkanemi don neman hadin kansu wurin kawo karshen rikici a jihar.

Sai ga ‘yan ta’adda sun kai farmaki jahar a yau Lahadi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here