Ina Kira da a yi Watsi da Kaiwa da Kawowa na Makiyaya Daga Sassan Arewa Zuwa Kudancin Najeriya – Gwamnan Kano

 

Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano ya bukaci a sanya dokar hana yawon shanu daga arewa zuwa kudu.

Ya ce za su samar da matsuguni ga makiyaya a dajin Samsosua da ke tsakanin jahar Kano da Katsina.

Ya ce hakan ne kawai zai iya sa a shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya a fadin kasar na Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ya dace a saka dokar da za ta hana kai shanu daga arewa zuwa kudu, The Cable ta wallafa.

A yayin zantawa da manema labarai bayan haduwarsa da gwamnonin APC tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, jahar Katsina, Ganduje ya ce idan har ba a hana yawon shanu ba, babu ranar kawo karshen manoma da makiyaya.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta shirya samar da wurin zama ga makiyayan a dajin da ke tsakanin iyakar Kano da Katsina.

Ya ce matsugunin zai kasance da gidaje, tafki, cibiyar dabbobi ta zamani da asibitocin dabbobi.

“Zamu gina matsugunin a dajin Samsosua, iyakarmu da Katsina kuma mun yi nasarar shawo kan illar ‘yan bindiga a yankin,” Ganduje yace.

“Za mu gina gidaje, tafkuna, cibiyar dabbobi, asibitin dabbobi kuma tuni muka fara ginawa makiyayan gidaje.

“Ina kira a kan a yi watsi da kaiwa da kawowa ko kuma yawon makiyaya daga sassan arewa zuwa tsakiyar kasar nan ko kudancin Najeriya.

“A saka dokar haramcin hakan ko kuma ba za mu iya shawo kan rikici tsakanin makiyaya da manoma ba kuma ba za mu iya hana satar shanu ba da ya addabe mu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here