Boko Haram: Kungiyar ta Kai wa Wasu Kauyuka Hari
Mayakan ta’addanci Boko Haram sun kai hari kauyuka uku na karamar hukumar Hawul.
Sun isa kauyukan uku da tarin yawansu a lokaci daya inda suka fara harbe-harbe.
An tabbatar da cewa sun kona majami’u 2 sannan mazauna kauyukan sun garzaya daji don tsira.
Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne a halin yanzu suna ragargazar kauyuka uku na karamar hukumar Hawul da ke jihar Borno, majiyoyi suka tabbatarwa Daily Trust.
An gano cewa maharan sun isa da tarin yawansu inda suka kaddamar da harin a kauyukan Tashan Allade, Shaffa da Khiributu dake karamar hukumar Hawul.
Daruruwan mazauna kauyen sun hanzarta barin gidajensu domin neman mafaka bayan sun ji harbe-harben.
Read Also:
An gano cewa mazauna kauyen sun shige dajikan da ke da kusanci da su domin samun mafaka.
Kamar yadda wata majiya daga ‘yan sa kai ta sanar, maharan sun kona majami’u biyu a Tashan Allade yayin da mazauna kauyen suke daji.
Wani daga cikin jami’an JTF, Balami Yusuf, ya bayyana cewa maharan suna ta ruwan alburusai a kauyukan Shaffa da Khiributu.
“A halin yanzu da muke magana, suna ta harbe-harbe. Kana iya jin karar. Muna daji kuma mutane tare da kananan yara suna ta kuka. Mun rasa yadda za mu yi,” Balami ya koka.
Idan za a tuna, mahara daga kungiyar ta’addancin sun kai hari kauyen Garkida da ke jihar Adamawa wacce ke da makwabtaka da karamar hukumar Hawul a jajiberin Kirsimeti.
Wannan harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 6 tare da konewar gidaje masu tarin yawa.