Shigar Boko Haram Abuja: Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Mariam Yusuf ta Musanta Batun
Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya ta musanta rade-radin shigar Boko Haram garin.
Kamar yadda kakakin rundunar, Mariam Yusuf ta sanar, a halin yanzu jami’an tsaro sun tsananta sintiri.
Ta tabbatar da cewa taron da aka yi na hukumomin tsaro na ranar Alhamis da ta gabata zai kawo karshen ta’addanci a FCT.
Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta musanta rade-radin da ake yi na cewa mayakan Boko Haram sun kai farmaki babban birnin kasar Najeriya.
Ana ta yadawa cewa Boko Haram sun kai hari Abuja bayan samun su da aka yi a jahar Neja dake makwabtaka da su, The Cable ta ruwaito.
Yusuf Mariam, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, ta ce an ga jama’a masu yawa a babura a wasu sassan babban birnin tarayyan, lamarin da ya kawo wannan rade-radin kuma yasa jami’ansu suna fita sintiri.
Read Also:
A wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi, Mariam tace an fara tsananta sintiri kuma hakan yana daga cikin matsayar da aka cimmawa bayan taron hadin guiwa na jami’an tsaro da aka yi a ranar Alhamis.
Ta ce:
“Hankalin jami’an tsaron hadin guiwa na FCT kan wata wallafa dake yawo wacce tace miyagun ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai hari babban birnin tarayya.
“Jami’an tsaron hadin guiwan na sanar da cewa babu gaskiya a cikin wannan wallafar kuma an yi ta ne domin gigita jama’a mazauna babban birnin tarayyan.
“Akasin wannan hasashen, shugabannin cibiyoyin tsaro na babban birnin tarayyan sun tashi domin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi garin kuma hakan yasa suka yi taro a ranar Alhamis, 29 ga watan Afirilun 2021.
“Kungiyar ta yanke hukuncin tura jami’an sintiri yankunan da matsalar tsaron ta fi addaba.
“Hukumomin tsaron sun fara aiki da babura, dawaki da sauran hanyoyin samo bayanai domin bankado dukkan matsalar tsaro ta babban birnin.”Bala Ciroma, kwamishinan ‘yan sandan jahar, yayi kira ga mazauna garin da su kwantar da hankulansu sannan su kasance masu kiyaye doka.