Hanyar da Shugaban Kasa da Gwamnoni Zasu bi, su Kawo Karshen Masu Satar Mutane – Sheikh Kabiru Gombe

 

Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya yi kira ga shugaban kasa da Gwamnoni.

Malamin ya ba masu mulki shawara su fito da kudi, su taimaka wa al’ummarsu da binci.

Shehin ya ce hakan ne hanya mai sauki da za a bi, a kawo karshen masu satar mutane.

Fitaccen malamin addinin nan, Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya duba halin da al’umma su ke ciki.

A wajen darashin tafsirin da yake gabatar wa, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya yi kira ga shugaban Najeriya ya buda baitul-malin gwamnati.

Kabiru Haruna Gombe ya bukaci shugaban kasa da kuma gwamnonin jahohi su fito da kudi da nufin ba talakawa kayan abincin da za su ci a watan azumu.

“A bude baitul-mali, a saya wa talakawa tireloli na kayan abinci; shinkafa ta rika yawo, ana ba talakawa.” “Ya ku gwamnonin jahohi, ku bude baitul-mali, a saya wa talakawa abinci a lokacin Ramadan.

A fitar da dukiyar talakawa, a saya masu abinci saboda Allah.”

Shararren malamin kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’at wa Iqamatus Sunnah ya ba gwamnatin kasar shawarar yadda za a magance matsalar satar mutane.

Sheikh Gombe ya ce: “Masu garkuwa da mutane sun addabe ku, su na ta kashe miliyoyi a kan tsaro domin ku tsare al’umma, amma har yau babu nasara.”

“Ga hanya mai sauki da za ku yi nasara, ku ji tausayin na-kasa, idan ku ka yi haka, Allah zai ji tausayinku.”

Sakataren na Jama’atul Izalatul Bidi’at wa Iqamatus Sunnah wanda aka fi sani da Izala, ya ce idan shugabanni su ka tausaya wa talakawansu, to Allah zai jikansu.

Malamin ya yi wannan bayani ne a tafsirin da yake gudanar wa na a bana tare da Alaranma Ahmad Sulaiman a masallacin ‘Yan lilo a Tudun Wada, Kaduna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here