‘Yan Boko Haram Sun Kashe Mutane da Dama a Kasar Nijar
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun tsallaka jamhuriyar Nijar tare da kashe mutane fiye da 70.
An kai harin ne a wasu kauyuka guda biyu da ke daura da iyakar kasar Nijar da Mali.
Kasashen nahiyar Afrika na fama da hare-haren ‘yan ta’dda da suka hada da Boko Haram, ISWAP, da ‘yan bindiga.
Read Also:
A ƙalla sama da fararan hula 70 ne aka kashe a wasu tagwayen hare-hare da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kan wasu ƙauyuka biyu dake ƙasar Nijar kusa da iyaka da kasar Mali.
Kimanin mutum 50 ne aka kashe a ƙauyen Tchombangou sannan 17 suka ji mummunan rauni kamar yadda wani jami’in tsaro ya tabbarwa Reuters ya kuma nemi da a sakaye sunansa, kamar yadda TheCable ta rawaito.
Wata majiya daga wani jami’in harkokin cikin gida na ƙasar ta Nijar da shima ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da an kashe sama da kimanin mutum 30 a Zaroumdareye.