Kungiyar Boko Haram ta Kashe Wasu Masu Saran Itace ta Kuma yi Garkuwa da Wasu
Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kashe masu saran itace uku, sun kuma sace wasu kimanin 40 a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Jami’an sa-kai a yankin sun faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an yi wa masu saran itacen tsinke ne a dajin Wulgo da ke kusa da kan iyakar Kamaru.
Da ma dai yankin sananne ne wajen ayyukan ‘yan ta-da-ƙayar-bayan, inda suke da sansanoni da yawa.
Read Also:
Masu faskaren sun je dajin Wulgo ne don neman itace amma ba su dawo ba har maraiace, abin da ya sa ‘yan gora suka bi bayansu, sai dai ba su ga kowa ba sai gawa uku da aka harba a baya.
“Ga dukkan alamu, duka mutum ukun an harbe su ne bayan sun yi yunƙurin tserewa saboda dakkansu an harbe su a baya,” a cewar wani shugaban ƙungiyar ‘yan gora a yankin.
An shafe tsawon lokaci babu layin salula a yankin sakamakon hare-haren da Boko Haram ta riƙa kaiwa tare da karya turakun layukan. Hakan ya tilasta wa mazauna yankin amfani da layukan Kamaru.
Mayaƙan Boko Haram na ƙara far wa masu saran itace da manoma, bisa zargin suna bai wa sojoji da ‘yan gora bayanai.
Hukumomi na gargaɗin masu faskare su guji shiga daji, sai dai rahotanni na cewa tilas ce ke sanya su yin hakan saboda an sare tsirrai a yankunan da ke da zaman lafiya.