Gwamnatin Jahar Borno Zata Kara Daukan Likitoci 40 Aiki
Gwamnan jahar Borno ya sake bada umarnin kara daukan likitoci don inganta asibitocin jahar.
Gwanman a baya ya ba da umarnin daukar ma’aikatan lafiya sama da 500 a jahar.
Gwamnanatin jahar ta kuma sayi wani fili a gaban wani asibiti don rage cunkoso a asibitin.
Gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Talata ya ba da umarnin daukar likitoci 40 a matsayin kari kan yardarsa da ya yi a baya, domin biyan bukatun kula da lafiya na karuwar al’ummar jahar, Vanguard News ta ruwaito.
Shawarwarin na ranar Talata na zuwa ne watanni hudu bayan da Gwamnan ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 594.
Read Also:
Daga cikin wadanda za a dauka sun hada da: likitoci lafiya 86, ma’aikatan jinya 365 da ungozomomi, masu harhada magunguna 45 da kwararrun masana kiwon lafiya 100 da sauran ma’aikatan tallafi.
Zulum ya sanar da amincewarsa ta baya-bayan nan ga daukar likitoci 40 bayan taron na ranar Talata tare da shugabannin gudanarwa na asibitocin gwamnati bakwai da cibiyoyin da ke da alaƙa da ke Maiduguri Metropolitan Council da ƙaramar hukumar Jere.
Taron, wanda aka gudanar a sirrance, ya ta’allaka kan inganta tsarin kiwon lafiya da kuma tabbatar da inganci da isar da aiyuka ga ‘yan kasa daidai da manufofin gwamnatin Zulum.
Bayan taron, Gwamna Zulum ya gudanar da aikin duba asibitin na Kwararru sannan ya ba da umarnin gina wani sashe domin rage yawan cunkoso a wasu wuraren.
Gwamnan ya kuma duba wani fili da Gwamnatin Jahar Borno ta saya da ke gaban asibitin kwararru, wanda za a yi amfani da shi domin fadada asibitin.