Gwamnan Borno Ya Gwangwaje Kananan Malamai da Sababbin Gidaje

Bayan ginawa manyan ma’aikata gidaje 20, gwamna Zulum ya sake gwangwaje kananan malamai.

Zulum ya gina wadannan gidaje cikin watanni 11 kacal.

Ya bada umurnin samar da shiri da zai baiwa ma’aikatan jami’ar daman mallakar gidajen kansu.

Gwamnan Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kaddamar da gidaje 50 da gwamnatin jihar ta gina domin jin dadin kananan ma’aikatan jami’ar Maiduguri.

An fara wannan ginin ne a watan Disamban 2019 kuma yana cikin ayyukan da gwamna Zulum ke yi domin jin dadin yan asaliin jihar Borno.

Wannan shine jerin gidaje na biyu da da gwamna Zulum ya ginawa manyan ma’aikatan jami’ar Maiduguri.

A Disamban 2019, ya kaddamar da gidaje 20 da ya ginawa manyan ma’aikatan jami’ar.

A bikin bude gidajen, Zulum ya bada umurnin biyan malaman jami’a da rikicin gwamnatin tarayya da ASUU ya shafa wasu kudade don rage radadi.

Gwamna Zulum ya umurci Sakataren gwamnatin jihar ya hada kai da bankin jihar wajen samar da wani shirin da zai tabbatar da cewa kananan ma’aikatan jami’ar sun mallaki gidajen kansu.

Bugu da kari, gwamnan ya bada umurnin sake gina tsangayar koyar da ilimin Injiniyanci kuma ya yi umurnin sayan kayayyakin da ake bukata wajen inganta sashen ilimin injiyancin gine-gine.

Bayan haka, Zulum ya yi kira ga ASUU su duba halin da jihar Borno ke ciki su sassauta yajin aikin da sukeyi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here