Gwamnatin Jahar Borno ta Nada Sabon Shehun Dikwa

Biyo bayan rasuwar Shehun Dikwa a makon da ya gabata, an nada sabon Shehun na Dikwa.

Gwamna Babagana Umaru Zulum ne ya nada sabon Shehun a wata sanarwa da aka fitar.

An nada Abba Umar Jato ne a matsayin sabon Shehun Dikwa a fadar jahar Borno Gwamnatin jahar Borno ta nada Abba Umar Jato a matsayin Shehun Dikwa, Daily Trust ta ruwaito.

Abba Umar Jato ya gaji marigayi Shehu Mohammed Ibn Shehu Masta II El-Kanemi, wanda ya rasu a makon da ya gabata.

Nadin nasa a matsayin mai fada aji na farko da Gwamna Babagana Zulum ya yi ya fito ne a cikin wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar.

Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Usman Jidda Shuwa ne ya sanar da rasuwar Marigayi Shehu a garin Biu, jim kadan bayan gabatar da ‘Staff of Office’ ga Sarkin Biu, Alhaji Mai Mustapha Umar Mustapha da Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi a ranar Asabar da ta gabata.

An dauke shi zuwa Abuja kwana daya kafin rasuwarsa a ranar Juma’ar da ta gabata.

Wannan shi ne karo na uku a jerin wadanda suka mutu a jahar cikin kankanin lokaci, bayan na Shehun Bama da na Sarkin Biu a shekarar 2020.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here