Brazil: Mutumin da Yafi Kowa Arziki a Kasar ya Rasu
Mashahurin attajirin Brazil dan asalin kasar Lebanon Joseph Safra, ya rasu ranar Alhamis ya na da shekara 82, a cewar bankin sa.
An haife shi a 1938 ga wasu iyalai Yahudawa a Beirut, ya yi hijira shi da Iyalan sa zuwa Brazil, inda mahaifin sa ya samar da inda ake kira Banco Safra.
Mutumin shine na 63 a jerin masu kudin duniya kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa.
Mashahurin attajirin Brazil dan asalin kasar Lebanon Joseph Safra, ya rasu ranar Alhamis ya na da shekara 82, a cewar bankinsa.
Read Also:
Safra, wanda kiyasin dukiyar ya kai kimanin $23.2 biliyan, wanda ya zo na 63 cikin jerin masu kudin duniya da mujallar Forbes ta fitar.
An haife shi a 1938 ga wasu iyalai Yahudawa a Beirut, yayi hijira shi da Iyalan sa zuwa Brazil, inda mahaifin sa ya samar da inda ake kira Banco Safra.
A 1962, shi da dan uwansa sun ci gaba da kula da bankin mahaifinsu, wanda ya rasu bayan shekara guda.
Sun maida shi babban cibiyar hada hada, in da ya fara aiki a kasashe fiye da 25.
Ya na son zayyana kuma mutum ne mai taimako, Safra ya sadaukar da wani bangare na dukiyar sa ga masu binciken lafiya, kuma ya sayi wasu aikin zayyana da adanawa a Sao Paulo’s Pinacoteca, wani babban gidan adana kayan tarihi a Brazil.