Zamu Bude Kofofin Samar da Abinci Ciki Sauki – Umakhihe
Sabon Sakataren Dindindin ya bayyana zuwansa don kawo cigaba a fannin samar da wadatar abinci.
Babbar Sakatariya Hajiya Karima ce ta mika masa takardun miki ayyuka a taron da akayi.
Daraktan yada labarai na Ma’aikatar Noma da Raya Karkara Theodore Ogaziechi ne ya fitar da sanarwar.
Sabon Sakataren din-din-din na Ma’aikatar Gona ta Tarayya, Earnest Afolabi Umakhihe, a jiya, ya yi alkawarin bude kofa ga manufofin samar da abinci cikin sauri, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Bayan ya karbi takaddun mikawa daga Babbar Sakatariya, Hajiya Karima Babaginda, wacce kuma Darakta ce a Ma’aikatar, inda ya bayyana karara cewa batun hadin kai da goyon baya daga daraktoci ba sai an sake jaddadawa ba don cimma manufofi mabanbanta na gwamnatin Buhari a bangaren noma.
Read Also:
Yace: “Na zo nan ne don gudanar da manufofin bayyanannu, koya daga daraktoci, kara daraja, da kuma daidaita al’amuran Ma’aikatar.
“Batun hadin kai da goyon baya daga daraktoci ba sai an sake jaddadawa ba domin cimma manufar Shugaban kasa game da yaduwa a bangaren aikin gona.”
A cewar sanarwar yayin maraba da Sakataren na Dindindin, Babbar SakatariyaHajiya Karima Babaginda, ta fada masa (Umakhihe) cewa Ma’aikatar tana da hurumin tabbatar da wadatar abinci da samar da ayyukan yi ga matasan kasar.
Ta yi alkawarin biyayya da jajircewar Daraktoci da dukkan ma’aikatan Ma’aikatar.
“Mr. Ernest Afolabi Umakhihe wanda aka haifa a ranar 5 ga Afrilu, 1964, ƙwararren Akanta ne na babban martaba, babban mai fasaha ne kuma fitaccen mai gudanarwa ne. Ya yi aiki a Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Waje, Ma’aikatar Tsaro, Ma’aikatar Wasanni, Ma’aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Tarayya na kasa,” ta kara da cewa.