Budurwa ta yi Wuff da Mahaifin Saurayinta

 

Wata budurwa ta haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan da ta bayyana hotunanta tare da mahaifin saurayinta.

An ce budurwar mai shekaru 23 ta dauki matakin mai ban mamaki ne bayan da ta kama saurayin nata da wata.

Ta hanyar auren mutumin mai shekaru 89, dangantakarta da tsohon saurayin nata ya sauya daga saurayi da budurwa zuwa da matar uba.

Wata budurwa ta auri mahaifin saurayinta mai shekaru 89 bayan da aka ce ta kama shi yana kulla alaka da wata ba ita ba.

Hoton budurwar mai shekaru 23 da mijinta tsofai-tsofai ya yadu a wani shafin Instagram mai suna The Savoy Show.

Da take mayar da martani ga cece-kucen jama’a da ke mamakin aikinta, budurwar ta caccaki mutanen da ke kiranta da munanan sunaye.

A cikin wani faifan bidiyo da kafar yada labaran ta wallafa, ta yi magana kan yadda saurayinta ya yaudare ta tare da neman mata daban-daban ciki har da kawayenta.

Ga dai abin da ta fadi:

“Don haka ake ta kirana da sunaye don na auri mahaifin tsohon saurayina, amma tsohon saurayina da ya yaudare ne ya nemi mata daban-daban ciki har da kawaye ba a kira shi da sunaye ba.”

Ra’ayoyin ‘yan soshiyal midiya

@stephenp12 ya ce:

“Abin ban mamaki ne!!!!! yanzu za ta zama kaka tana lura dan rikonta wanda a zahiri a baya tsohon saurayinta ne…”

@jay_west.42 ya ce:

“Don kawai ya aikata abin da ya yi, ba yana nufin abin da kika yi daidai ba ne! Me ya sa mata suke kokari su daidaida halayensu ta hanyar kwatanta kansu da mazan da suka ce sun fi?!”

@lashaunhaywood said:

“Yana da shekaru 89 da dala miliyan 90 wannan shi ne dalilin da ya sa amma kaji bana jin haushin ta fa.”

@tiptoez ya ce:

“Ya yaudari mata da yawa, wasu daga cikinsu “abokai na ne” akwai alamar tambaya.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here