Shugaba Buhari ya Nada Sababbin Shugabanni a Hukumar NASENI

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sababbin Darektocin NASENI.

Sanarwar nadin mukamin ya fito ne kafin aji labarin zai bar Najeriya a dazu.

Olayinka Adunni Komolafe ce ta zama sabuwar Darektar hukumar NASENI Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sababbin shugabanni a hukumar NASENI mai kula da kirkiren kimiyya da fasaha a Najeriya.

Shugaban kasar ya yi wannan sauya-sauye ne a yunkurin gwamnatin tarayya na ganin an gyara wannan ma’aikata domin ta yi aiki da kyau.

Nadin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ya fito ne ta ofishin babban ma’aikacin fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim A. Gambari.

Daily Trust ta ce an sa hannu a wasikar Ibrahim A. Gambari ne a ranar 24 ga watan Maris, 2021.

Jaridar ta ce fadar shugaban kasa ta sanar da shugaban ma’aikatar NASENI game da wannan nadin mukamai da mai girma shugaban kasa ya yi.

Kamar yadda ma’aikatar ta NASENI ta bayyana a wani jawabi da ta fitar a ranar Litinin, wasikar shugaban kasar ta samu shigo wa hannunta.

Mai magana da yawun bakin NASENI, Olusegun Ayeoyenikan ya bayyana haka a wata sanarwa.

Wadanda aka nada su ne: Dr. (Mrs.) Olayinka Adunni Komolafe, sakatafiyar ma’aikatar, sai Injiniya Farfesa Danshehu Bagudu Gwandangaji. Sai kuma Farfesa Umar Ibrahim Gaya, Misis Nonyem Onyechi, da Mista Ibrahim Baba Dauda. Darektcoin za su kula da harkar fasahan, gudanar wa, tsare-tsare, cigaban kasuwanci, da harkar kudi.

Za su yi shekara biyar a wannan kujeru.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here