Shugaba Buhari ya Aminci da Bude Sabbin Polytechnic a Jahohi 3

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bude wasu sabbin Polytechnic guda uku a cikin wasu jihohi don saukaka wa mutane samun karatun gaba da sakandare.

Darektan watsa labarai da hulda da jama’an Ma’aikatar Ilimi, Mr Ben Bem Goong ya bayyana hakan ta wata takarda da ya saki a Abuja.

A takardar ta ranar Talata ya ce Polytechnic din guda uku sun hada da na Umunnoechi a Jihar Abia, Orogun a Jihar Delta da kuma Kabo a Jihar Kano.

Abuja-Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bude Kwalejojin Fasaha (Polytechnic) guda uku na tarayya a bangarori daban-daban na kasar nan a matsayin hanyar saukaka wa jama’a damar samun ilimin gaba da sakandare.

A wata takarda wacce Darektan watsa labarai da hulda da jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta tarayya, Mr Ben Bem Goong ya saki a ranar Talata a Abuja ya shaida hakan.

A cewarsa Polytechnic din guda uku sun hada da na Umunnoechi da ke Jihar Abia, Orogun da ke Jihar Delta da Kabo a Jihar Kano, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Mashawarcin shugaban kasa a bangaren kafafen watsa labarai na zamani, Bashir Ahmad shima ya tabbatar da rahoton kafa kwalejojin uku a shafinsa na Twitter.

Za su fara aiki a watan Oktoba mai zuwa

Nigerian Tribune ta nuna inda ya ce sabbin kwalejin na Fasaha din za su fara aiki ne a watan Oktoban 2022.

Idan aka tattara, yanzu haka akwai Foliteknik guda 36 na tarayya da ke cikin Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here