Shugaba Buhari ya Amince da Naɗin Sababbin Alƙalai 18 a kotun Daukaka ƙara
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin alkalai 18 na kotunan daukaka kara a Nigeria, The Cable ta ruwaito.
Kwamitin Kolin Shari’a ta Kasa, CJN, Karkashin jagorancin Ibrahim Muhammad, Alkalin Alkalan Nigeria, CJN, a watan Maris ya mika sunayensu ga shugaban kasa domin a musu karin girma.
A cikin wasikar da ya aike wa CJN din, Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya ce Buhari ya amince da bukatar yi wa alkalan karin girma.
Read Also:
“Ina farin cikin sanar da kai cewa Mai girma Shugaban kasa ya amince da nadin wadannan a matsayin alkalan kotun daukaka kara saboda matayinsu a kotun kamar yadda ya ke a sashi na 237 da 238 na kundin tsarin mulkin 1999,” a cewar wasikar.
Shugaban kasar ya kuma yi wa sabbin alkalan da aka nada fatan alheri a yayin da za su cigaba da ayyukansu a kotunan daukaka kara.
Ga jerin sunayen alkalan:
1 Bature Isah Gafai
2 Muhammad Ibrahim Sirajo
3 Waziri Abdul-Azeez
4 Yusuf Alhaji Bashir
5 Usman A. Musale
6 Jauro Ibrahim Wakili
7 Abba Bello Mohammed
8 Mohammed Danjuma
9 Danlami Zama Senchi
10 Mohammed Lawal Abubakar
11 Hassan Muslim Sule
12 Amadi Kenneth Ikechukwu
13 Peter Oyinkenimiemi Affen
14 Sybil Onyeji Nwaka Gbagi
15 Olasumbo Olanrewaju Goodluck
16 Banjoko Adebukunola Adeoti Ibironke
17 Olabode Abimbola Adegbehingbe
18 Bola Samuel Ademola