Rashin Idris Deby Zai Iya Haifar da Matsalar Tsaro a Najeriya – Ministan Tsaro

 

Ministan tsaro ya ce mutuwar Idris Deby matsala ce ga masu makwabta da Chadi.

Bashir Magashi ya ce babu kasar da za ta koka da rashin Idris Deby irin Najeriya.

Janar Magashi ya tabbatar cewa gwamnati za ta tabbatar da zaman lafiya a Chadi.

A ranar Alhamis, Ministan harkar tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya yi magana game da kashe shugaban Chadi, Idriss Deby, da aka yi.

Janar Bashir Magashi ya bayyana cewa kisan Idriss Deby zai iya jawo wa Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da Chadi, matsalolin tsaro.

A dalilin haka gwamnatin tarayya ta ce ta inganta tsaro domin a tabbatar da wanzurwar zaman lafiya, kuma ta na bibiyar kasar da ta ke kan iyakarta.

Jaridar Punch ta ce Janar Bashir Magashi ya yi magana ne a fadar Aso Villa a wajen taron mako-mako da ma’aikatan fadar shugaban kasa su ke shirya wa.

Ministan ya ke cewa:

“Da mu ka ji labarin takaicin kashe shugaban kasar Chadi, mun san cewa matsala za ta iya auku wa a kasashen da ke makwabtaka da ita.”

“Najeriya ce za ta fi gamuwa da matsala sosai a dalilin rashinsa (Idriss Deby)” inji Janar Magashi.

“Idan akwai matsalar tsaro a Chadi, za a samu matsaloli sosai.

Amma mun gode wa Ubangiji, sojojinmu da yawa su na sintiri a Chadi, Nijar da Kamaru.”

“Duka kasashen nan har da Chadi sun bada gudumuwa sojoji a cikin dakarun hadin-gwiwa.”

A cewar Janar Magashi, an dauki matakan da za su magance matsalolin da za iya samu a Najeriya, ya ce za a tsare iyakoki domin a hana barkowar jama’a.

“Amma ina tabbatar maku, mu na sane da iyakokinmu, mun san da abin ke faru wa, gwamnati ta na bakin kokarinta na ganin samu zaman lafiya a Chadi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here