Rashin Tsaro: Buhari ya Amince da Zama da ‘Yan Majalisar Wakilai
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da zama da ‘yan majalisar wakilai nan kusa.
Hakan ya biyo bayan yadda ‘yan majalisar suka rude, suka kidime kuma suka gigice.
Majalisar ta dauki zafi a ranar Talata bayan an kawo batun kashe-kashen manoma 43 na jihar Borno.
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da zama da ‘yan majalisar wakilai don tattaunawa a kan matsalar rashin tsaro, kamar yadda ‘yan majalisar suka bukata.
Kamar yadda kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila yace, an tsayar da ranar da za a tattauna, kuma nan kusa za a sanar da lokacin.
Read Also:
Ya fadi hakan a ranar Laraba, inda yace Shugaban kasa ya fi kowa shiga cikin damuwa a kan yanayin rashin tsaron da kasarsa take ciki, kuma zai yi wa ‘yan Najeriya magana ta wurin wakilansu nan kusa.
Shugaban kasa ya yanke wannan shawarar ne a ranar Talata lokacin da majalisar ta dauki zafi a kan kashe-kashen manoman shinkafa 43 na jihar Borno, wanda ‘yan Boko Haram suka aiwatar.
Bayan kawo maganar majalisa, duk ‘yan majalisar suka kidime kuma sun rude, kowa yana tofa albarkacin bakinsa.
Ganin hakan ne kakakin majalisar yace ba zai kyautu a yanke wani hukunci a kan harkar tsaro ba, ba tare da tuntubar shugaban kasa ba.
Kakakin ya kwatanta wannan taro da za a yi a matsayin cigaba, wanda kowa yake sa ran ganin nasara, Channels TV ta wallafa.