Shugaba Buhari ya Miƙa Saƙon Ta’aziyyarsa ga Iyalan Waɗanda Hatsarin Kwale-Kwale ya Rutsa da su a Anambra
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin sake yin duba don inganta matakan kiyaye afkuwar haɗurra a tsarin sufurin ruwa na ƙasar, sakamakon hatsarin wani kwale-kwale da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a jihar Anambra.
An samu rahotanni masu cin karo da juna kan ainihin yawan waɗanda abin ya rutsa da su a jihar da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Amma wata sanarwa da mai taimaka wa Buhari kan yada labarai ta ce, ana jiran bayanai har yanzu, sai dai hukumimin agaji sun tabbatar d acewa “yawan waɗanda suka mutu ya kai 76.”
Yawancin waɗanda suka rasun dai mata ne da yara da suke ƙoƙarin tsere wa yankinsu da ambaliyar ruwa ta mamaye.
Read Also:
Rahotanni sun ce jirgin wanda ke ɗauke da mutum fiye da 80 ya yi hatsarin ne a yankin Ogbaru a ranar Juma’a.
Jami’ai sun ɗora alhakin jawo hatsarin kan injin jirgin da suka ce ya lalace, sannan kuma jirgin ya yi karo da wata gada.
Shugaba Buhari ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya rutsa da su, yana mai bayyana hatsarin a matsayin mummuna, sannan ya ƙara da cewa dole ne hukumomi su yi duk abin da ya dace don gano waɗanda har yanzu ba a gansu ba.
Kazalika shugaban ya bai wa hukumomin gwamnati umarnin sake yin nazari kan tsarin tabbatar da tsaro a sufurin jiragen ruwa da kwale-kwale don kare afkuwar irin hakan a gaba.
Ana yawan samun hatsarin kwale-kwale a Najeriya – inda a mafi yawan lokuta ake ɗora alhakin hakan kan ɗaukar mutanen da suka fi ƙarfin jirgin da sauran matsaloli.