Shugaba Buhari ya Bukaci Majalisa da ta Tabbatar da Tantance Farfesa Omotayo a Matsayin Darakta-Janar na NIPSS

 

The Nation ta rawaito cewa, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da tantance Farfesa Ayo Omotayo a matsayin Darakta-Janar na Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta NIPISS da ke Kuru, kusa da Jos, Jihar Filato.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar bukatar Buhari a zauren majalisar bayan dawowa daga hutun aiki na kwanaki 18 na Sanatoci domin baiwa ma’aikatu hukumomi (MDAs) kare kudirinsu na kasafin kudin 2022.

Shugaban a cikin wasikar ya ce nadin Farfesa Omotayo a matsayin babban jami’in NIPISS ya kasance daidai da sashe na 5 (2) na dokar NIPSS ta 2004.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here