‘Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kona Gidaje da Dukiyoyin Jama’a a Garin Askira Uba da ke Borno
Rahoto ya bayyana cewa, wasu miyagun ‘yan ta’addan Boko Haram sun fatattaki wani kauye a jahar Borno.
A halin da ake ciki, sun fatattaki kowa a garin, lamarin da jawo asarar dukiyoyi da kone gidaje masu yawa.
An ce sojoji sun fita da sarkin garin, duk da haka mutane sun fara dawowa bayan lafawar harin na Boko Haram.
Borno – Mazauna garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba a jahar Borno sun tsere lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari wani kauye ranar Laraba.
Daily Trust ta ce ta samu labari daga majiyoyi cewa ‘yan ta’addan da suka kai harin da safe sun kona gidaje da dama.
Wani ganau ya ce maharan sun kai farmaki a yankin Krangla, mai tazarar kilomita takwas da garin.
Read Also:
Yayin da wasu mazauna yankin suka tsere zuwa cikin daji da kuma tsaunuka da ke kewaye domin tsira da rayukansu, rahotanni sun ce jerin gwanon sojoji sun yi wa basaraken yankin rakiya daga wajen garin.
Bulama Jonah, daya daga cikin iyayen ‘yan matan Chibok da aka sace, ya ce ya tsere daji da wasu mutane da dama inda suka boye har lamarin ya dan lafa.
Ya ce:
“Mun garzaya daji domin tsira; kowa yana gudu ne kawai saboda mun ji sun kona Krangla kuma suna tafiya zuwa Askira.”
“Mun dawo garin, duk da cikin tsoro, bayan mun ji sojoji sun shiga domin su tare su kafin su isa nan. Har yanzu sojoji suna nan.”
Wani direba dan kasuwa da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce da jim maharan na kan hanyarsu, sai ya gudu da matarsa mai ciki.
A ranar Litinin din da ta gabata The Cable ta rawaito yadda ‘yan Boko Haram suka yi musayar wuta da sojojin Najeriya duk dai a jahar ta Borno.