Shugaba Buhari ya Nuna Damuwarsa Kan Rashin Tsaro

 

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanar da bakin ciki da yake shiga idan aka samu rashin tsaro.

Ya ce kamar yadda iyaye da marikan yara ke jin takaici, haka yake shiga tashin hankali idan aka samu karantsayen tsaro.

Ya yi kira ga masu kishin kasa da taimaka wa sojoji wurin samar musu da bayanan sirri don kawo karshen rashin tsaro.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana matukar shiga takaici da bakin ciki in har aka samu rashin zaman lafiya da karantsaye a kan tsaro a kasar nan.

Shugaban kasan a sakonsa na Kirsimeti ga ‘yan Najeriya ya yi kira garesu da su bada goyon baya ga dakarun soji da sauran hukumomin tsaro.

“Da gangan ba zan ki sauke babban nauyin da ke kaina ba na tabbatar da tsaron rayuka da kadadrori ba. Ina shiga halin takaici matukar aka samu karantsaye a fannin tsaron kasar nan.

“Na kan shiga halin damuwa fiye da matasa. A yanzu an fi saka wa ‘yan makaranta ido kuma ‘yan ta’addan nan suna mayar da su hanyar tada hankulan al’umma.

“A matsayina na uba, ina samun tashin hankali tare da alhinin da iyaye tare da marika ke shiga idan yaransu suka fada hannun makiyan al’umma.

“Ina rokon sauran masu kishin kasa da su bai wa dakarun soji da sauran hukumomin tsaro goyon baya da hadin kai ta hanyar samar da bayanan sirri domin kakkabe dukkan ‘yan ta’adda da ke damunmu,” wani sashi na takardar ya sanar.

Ya dauka alwashin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da bai wa dakarun soji dukkan goyon baya da suke bukata, Daily Trust ta wallafa.

Ya horesu da su mayar da hankali wurin kawo karshen rashin tsaron da ya addabi jama’a.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here