Shugaba Buhari ya Fara Killace Kansa 

 

Bayan shafe sati daya a New York, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya tare da mukarrabansa.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya bayyana dalilin da ya sa Buhari da mukarrabansa suka fara killace kansu bayan tafiyar.

Keɓewar kwanaki 5 da Shugaban kasar ya shiga ya yi daidai da ƙa’idodin Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC).

FCT, Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara killace kansa bayan dawowarsa daga taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na 76 daidai da ka’idojin tafiye-tafiye na COVID-19.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya tabbatar wa PM News ci gaban a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba.

A cewar Adesina, shugaban kasar da hadiman da suka yi masa rakiya zuwa Amurka sun shiga killace kansu tun bayan dawowar su a ranar Lahadi, 26 ga Satumba.

An bayyana hakan ne bayan rashin bayyanar Buhari a taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ci gaba da cewa Buhari zai gama killace kansa a ranar Alhamis, 30 ga watan Satumba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here