Shugaba Buhari ya Gana da Iyalan Wadanda Suka Mutu Sanadiyyar Fashewar Nakiya a Kano

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan uwan wadanda suka mutu sakamakon fashewar nakiya da ya faru a Kano.

Shugaban wanda ya ziyarci Kano domin halartar taron makon sojojin saman Najeriya, ya gana da ‘yan uwan mutum 9 da suka rasu a fadar Sarkin Kano, inji rahoton Daily Trust.

Buhari ya jajanta wa iyalan da Sarki da gwamnatin jihar Kano kan wannan mummunan lamari, wanda ‘yan sanda suka ce fashewar iskar gas da wani sinadarai ne amma daga baya suka sauya batu.

Da yake jawabi tun da farko, gwamnan na Kano ya ce gwamnati ta bayar da Naira miliyan 9 a matsayin diyya ga iyalan wadanda suka rasu yayin da aka ba mutane 10 da suka samu munanan raunuka Naira miliyan 2.

Hakazalikam an ba da Naira miliyan daya ga wadanda suka samu kananan raunuka su raba.

Gwamnan ya kuma ce wata cibiyar kasuwanci mai suna African Centre da fashewar ta shafa an ba su Naira miliyan 2 yayin da kuma Winners Academy da dalibanta suka samu raunuka sakamakon fashewar gilashi ta samu Naira miliyan daya.

A nasa bangaren, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gode wa shugaban kasar bisa wannan karimcin da ya nuna, inda ya ce jama’ar Kano ba su yi mamakin ziyarar shugaban ba, domin kuwa shi (Buhari) ya kasance na talakawa.

Ya yi addu’ar Allah ya sa shugabanni masu gaskiya su fito a gaba Najeriya a lokacin babban zabe mai zuwa ya ke tunkarowa. Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here