‘Yan Bindiga Sun Kona Ofishin ‘Yan Sanda Tare da Kashe Mutane 4 a Anambra

Tsagerun ‘Yan bindiga a Anambra sun kashe mutane hudu a wani farmaki da suka kai wurare daba-daban a jihar.

Hakazalika, ‘yan bindigar sun kona ofishin yan sanda da motocinsu a yankin Anaku da ke karamar hukumar Ayamelum ta jihar.

Zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin yan sandan jihar ba kan lamarin domin kakakin rundunar ya yi gum da bakinsa.

Anambra- Bayan kashe mutane bakwai da suka yi a jiya Lahadi, 22 ga watan Mayu, tsagerun ‘yan bindiga sun sake kashe wasu mutum hudu a wurare biyu a jihar Anambra.

Maharan sun kuma farmaki wani ofishin yan sanda a garin Anaku da ke karamar hukumar Ayamelum sannan suka kona motocin da ke wajen, Vanguard ta rahoto.

An tattaro cewa kashe-kashen da aka yi, ya wakana ne a garin Ogbunike da ke karamar hukumar Oyi.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun farmaki kasuwar shanu da ke yankin.

An kuma kashe wani mutum daya a garin Peter Obi na Agulu a karamar hukumar Anaocha, inda aka kuma kona wata motar sintiri.

Kakakin yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, ya ki cewa komai kan lamarin, amma wata majiya ta yan sanda ta tabbatar da faruwar harin na Anaku.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here