Shugaba Buhari ya Gana da Gwamnan Borno a Fadarsa

 

Farfesa Babagana Umara Zulum, gwamnan Jihar Borno, ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa.

Fadar shugaban kasa da ofishin gwamna Zulum basu fitar da sanarwa dangane da ganawar ba ya zuwa yanzu.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a fadarsa, Villa, wacce ke Aso Rock a birnin tarayya, Abuja.

Hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau, ya wallafa hotunan ziyarar da Farfesa Zulum ya kai wa Buhari a fadarsa. Sai dai, Sallau bai yi karin bayani a kan dalilin ganawar ba.

Kazalika, fadar shugaban kasa ko ofsihin gwamna Zulum basu bayyana dalilin ganawar ba ya zuwa yanzu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here