Shugaba Buhari ya Shiga Ganawar Sirri da Gwamnoni 7 a Fadarsa

Yayin da jam’iyya mai mulki ke cigaba da faɗi tashin zakulo mataimakin shugaban ƙasa, gwamnonin sun dira fadar Buhari.

Yanzu haka shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya shiga ganawar sirri da aƙalla gwamnoni Bakwai a fadarsa ranar Talata.

Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, Gwamnonin Kaduna, Filato, Nasarawa, Imo, Kogi. Jigawa da Borno sun samu halarta.

Abuja – Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shiga taron sirri yanzu haka da gwamnonin APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban gwamnonin da suka ɗare kan madafun iko a APC, Gwamna Atiku Bagudu, na jihar Kebbi, shi ne ya jagoranci takwarorinsa zuwa wurin Buhari.

Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC ke cigaba da faɗi tashin zakulo mataimaki ga ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Mutanen da suka halarci taron

Taron wanda ke gudana yanzun ya samu halartar shugaban ma’ikatan fadar gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnati, Boss Mustapha.

Haka nan kuma a ɗaya ɓangaren gwamnonin da suka je wurin taron sune, Babagana Zulum na Borno, Nasir El-Rufai na Kaduna, Abdullahi Sule na Nasarawa, Badaru Abubakar na Jigawa.

Sauran sune, gwamna Simon Lalong na jihar Filato, Yahaya Bello na jihar Kogi da kuma gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.

Channels TV ta ruwaito cewa duk da babu cikakken bayani kan dalilin taron amma ya zo ne mako ɗaya bayan kammala zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa.

Su wa ake tsammanin zaben mataimaki daga cikin su?

Rahoto ya nuna cewa tsohon gwamnan Legas ɗin ya rubuta sunan tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima, wanda ya taka rawa wajen nasararsa a matsayin wanda ya ke son ya zama mataimaki.

Mambobin tsohuwar jam’iyyar CPC da ta cure zuwa APC, suna shirin gabatarwa Buhari da sunan Abubakar Malami da Hadi Siriki don zaɓar ɗaya ya zama mataimaki.

Tsohon sakataren gwamnati, Babagana Kingiɓe, wanda ya kasance mataimaki ga MKO Abiola a zaɓen 1993 ya tura sunayen mutum uku ga Tinubu domin duba wa.

Mutanen sun haɗa da gwamna Babagana Umaru Zulum, mataimakiyar shugaban majalisar ɗinkin duniya, Amina J Muhammed, da kuma Kashim Ibrahim-Imam.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here