Babban Abin kunya ne Ace shugaba Buhari, a Matsayin Tsohon Soja, ya Gaza Magance Rashin Tsaro – Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya kara sukar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, akan harkar tsaro.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya kara sukar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, akan harkar tsaro.
A cewar Obasanjo, babban abin kunya ne ace shugaba Buhari, a matsayin tsohon soja, ya gaza magance rashin tsaro
Obasanjo ya bayyana cewa akwai banbanci a tsakanin Buharin yanzu da tsohon Buharin da ya sani
Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya soki shugaba Muhammadu Buhari akan harkar tsaron ƙasar nan.
Read Also:
Mr Obasanjo, ya ce, abin takaici ne yadda shugaban kasa mai matsayin babban hafsan hafsoshin kasar nan ya gaza kawo karshen yan tayar da ƙayar baya.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi wannan furuci ne jiya Lahadi da masanin tarihin nan, Toyin Falola, inda ya buƙaci shugaban ƙasa mai ci da ya farka daga dogon baccin da yake yi.
Kodayake ya nuna rashin yardarsa kan iƙirarin cewa ba shugaban ƙasar ba ne ke juya kujerar mulkin ƙasar.
“Zan iya cewa na san Shugaba Buhari saboda ya yi aiki da ni. Amma sau da yawa na kan tambayi mutane, shi ne ko kuwa ya canza ne daga Buhari da na sani? Ban yarda da maganar mutane cewa wannan Buhari daga Sudan ya ke ba, duk da wannan shirmen” in ji jaridar Premium Times.
“Amma da abin da nake gani, na yi imani watakila zai yi tunanin abin da ya gada. Wataƙila zai ɗau darasi daga abin dake faruwa yan kwanakin nan. Idan kai babban kwamanda ne ana samun tashe tashen hankula na faruwa, to ya kamata ka farka,” a cewarsa.